Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Halin da na samu Sambo Dasuki tsare a hannun DSS -Jones Abiri




Cikin wata tattaunawa ta musamman da PREMIUM TIMES ta yi da dan jaridar nan da ya shafe shekaru biyu a tsare a hannun SSS da a yanzu aka fi sani da DSS, bayan ya fito, Jones Abiri ya bayyana irin zaman kuncin da ya yi a tsare, kuma ya bada labarin irin halin da ya samu tsohon mai bada shawara a kan harkokin tsaro, na lokacin Goodluck Jonathan, Sambo Dasuki ke ciki.
PT: Ko ka samu yin katarin ganin Sambo Dasuki a inda SSS suka tsare ka a Abuja kuwa?
ABIRI: Tabbas na hadu da Sambo Dasuki amma fa ba a daki daya aka tsare mu ni da shi ba. Kun san su ai manya ne. Amma fa duk da haka ina tabbatar muku da cewa a inda ya ke a tsare yanzu ko wurin bayan gida babu. A duk lokacin da ya matsu, sai dai su fito da shi su kai shi wani wuri can daban.
To ta wannan dalili ne har mu ke iya ganin sa idan an fito da shi zai dan zagaya ban-daki. Amma akwai ma lokacin da mu ka hadu gaba da gaba, har ma na mika masa hannu muka gaisa. A lokacin ya fito ne zai je ban daki, ni kuma ina tsaye a wajen dakin mu.
A inda na ke tsaye a lokacin da na gan shi har muka gaisa, can ne ake fara ajiye wanda aka kamo, bayan an yi masa bincike, daga nan kuma sai a fara karkasa ku cikin dakunan gadurum a ci gaba da tsare ku.
Saboda na rigaya na san batun tsare shi da aka yi, da kuma dalilin tsare shin da ake yi, shi ya sa ban ma tsaya yin wata magana da shi ba.
PT: To kai a dakin da aka tsare ku akwai ban-daki a ciki ne?
ABIRI: Gaskiya akwai ban daki kam.
PT: To idan wanda ake tsare da shi ba ya lafiya, a nan cikin gadurum ake kula da lafiyar sa, ko kuma ana fita waje zuwa asibiti domin a duba shi?
Abiri: Wasu lokuta likita ne kan zo ya duba masara lafiya. Amma fa sai idan ta kama sannan ne a kan an fita da wani zuwa asibiti. Idan ba haka ba, sai dai likita ya zo ya buba, ya rubuta magani, a kawo maganin ga wanda aka tsare din.
PT: Ya a ka kwatanta dakin da aka tsare ku?
ABIRI: Dakin dai ba wani fadi gare shi can ba, domin bai ma kai fadin wani babban falo ba. Kuma mu 26 ne a tsare cikin sa. A kan tsandaurin daben tayil mu ke kwanciya. Sai fa wani lokaci can da muka roki a kawo mana kwali mu farke domin mu rika dora kan mu a kan kwalin, shi ne aka yi mana wannan alfarmar, har mu ka rika yin matashin kai da kwali.
Sannan kuma babu wadataccen iska, domin dakin a karkashin kasa ya ke. Kuma wata fanka ce guda daya tal ke ba mu iska, duk kuwa da yawan mu. Akwai taga, amma kamar babu ce, tunda inda mu ke ba mu jin kadawar iskar da ke yawo sarari, ballantana har ya shigo mana ta taga.

Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies