Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi zargin cewa barayin da suka sace kudin kasar sun sake daura damarar komawa kan mulki bayan sun sha kaye a zabukan da suka gabata.
Wata sanarwa da mai rokin mukamin kakakin jam'iyyar Mr. Yekini Nabena ya fitar anar Lahadi ta ce babu abin da barayin ke son yi illa sake kassara Najeriya.
"Muna jawo hankalin 'yan Najeriya bisa shirin da wasu 'yan siyasa ke yi na sayen kuri'u da kuma yin amfani da su ta hanyar da bata dace ba da zummar tauye hakkin masu kada kuri'a a zabukan da ke tafe," in ji sanarwar.
Sai dai Mr. Nabena bai bayar da wata hujja da ta nuna gaskiyar ikirarin da ya yi ba.
A cewar sa, "mutanen su ne suka wawure kudaden jama'a domin gudanar da harkokin siyasarsu kamar yadda ya gabata a gwamnatocin da suka gabata, don haka dole a hana su kwata hakan a zabuka masu zuwa."
Mai magana da yawun jam'iyyar APCn ya ce a cikin shekara uku gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta tsallake duk wasu gwaje-gwaje na mizanin auna rashawa da hukumomin da ke yaki da cin hanci suka shata, abin da, a cewar sa, ya haifar da sakamako mai kyau.
Ya ce a kwanakin baya-bayan nan 'yan hamayya sun yi amfani da kafafen watsa labaran Najeriya wurin kaddamar da shelar kin jinin yaki da cin hancin da ake yi da zummar durkuar da kasar.
Sai dai masana harkokin siyasa na ganin Mr. Nabena ya fitar da sanarwar ce domin cimma manufar siyasa.
A cewar su, akwai jami'an gwamnatin APC da dama da ake zargi da cin hanci amma an kawar da kai daga gare su saboda ba 'yan hamayya ba ne.
Hasalima, babbar jam'iyar hamayya, PDP, da wasu 'yan kasar na zargin ana yaki da cin hanci ne kawai da mutanen da ba a dasawa da su, suna masu cewa da zarar mutum ya koma jam'iyya mai mulki ba a sake waiwayar zarge-zargen da ake yi masa na rashawa, sai dai idan ba ya dasawa da gwamnati.
APC da fadar shugaban kasa sun sha musanta hakan.
0 komentar:
Post a Comment