
Fim din ta kashe shi, fim ne da Jamilu Ahmad Yakasai ya shirya, kuma har sun fara sayar dashi a kasuwa. A labarin dai, kamar yadda aka ji a gaske, wata mata ce tsananin kishi ya sanya ta kashe mijinta yana cikin sallah, saboda zai karo mata kishiya. Masu hada fim din na fata ne su fadakar da jama'a kan mugun kishi da abin da zai tarwatsa ma mutum rayuwa.
A waje daya kuma, wasu na gani tunda batun yana kotu, bai kamata ayi fim din ba, ko ma kuma cewa wani ya rasa ransa a gaske, bai kamata ayi ffim a ci riba dashi ba.
Daga naijhausa
0 komentar:
Post a Comment