
Wani hoton 'yar sarkin Saudiyya Gimbiya Hayfa bint Abdullah al-Sa'ud, da aka buga a bangon mujallar Vogue ta watan Yuni yana ci gaba da jan hankalin mutane sosai. A hoton dai Gimbiya Hayfa ta sa fararen kaya tana zaune a cikin wata haddadiyar mota a hamada. Mujallar, ta bayyana zaman kasaitar da Gimbiyar ta yi a cikin motar da kuma yadda ta rike sitiyarin cike da bajinta, tana mai alakanta hakan da irin sauye-sauyen da ake ci gaba da samu a kasar ta Saudiyya. Sai dai ba a ambato barazanar da matan da suka yi fafutukar ganin an kyale mata su tuka mota ke fuskanta ba. Masu fafutikar ba mata damar tuki a Saudiyya na fuskantar barazana Saudiyya za ta zuba jarin $64bn a bangaren nishadantarwa Ana ce-ce-ku-ce kan nuna mata 'yan kokawa a Saudiyya An tsare wasu mutane masu mahimanci da dama bayan da aka umarce su da kar su yi magana game da batun, duk kuwa da cewa ranar da Saudiyya ta sa don bai wa mata damar su fara tuka mota na kara karatowa. Masu fafutuka a Saudiyya sun soki mujallar Vogue da kin yin bayani kan irin batun da ya shafe su, da kuma bayyana Gimbiya Hayfa a matsayin wacce ta fi yin hobbasa wajen nema wa matan kasar samun 'yancin tukin mota al'amarin da bai yi wa masu rajin dadi ba. Wani dan kasar ya ce abun ya yi matukar ba su takaici dangane da yadda mujallar ta Vogue Arabia ta nuna kamar gimbiyar ce amara wajen neman wannan 'yanci ba tare da nuna kokarin masu fafutukar ba. Kasar Saudiyya ta sanar da cewa daga ranar 24 ga watan Yuni, matan kasar za su sami izinin fara tukin mota a cikin daular. Wannan matakin zai kawo karshen hanin tukin mota na shekaru masu yawa a kasa ta karshe a duniya da ta hana mata tukin mota. Hukumomi sun dauki wannan matakin na kyale matan Saudiyya su fara tukin mota a bara ne. Kuma a watan Yunin bana aka shirya fara amfani da dokar - amma sai yanzu aka bayyana ainihin ranar da mata za su fara kam kambun motoci. Wannan matakin shi ne mafi jan hankula a cikin dukkan matakan kawo sauyi da Yarima mai jiran gado Muhammad bin Salman ya dauka a cikin kasar.
0 komentar:
Post a Comment