An bayyana fara jawo ruwan teku daga kudancin Nijeriya zuwa arewa da gwamnatin Muhammadu Buhari ta fara da cewar abin a yaba wa gwamnatin tarayya ne kwarai da gaske.
Alhaji Haruna Rabi’u Jega, wani fitaccen mai sana’ar sayar da kifin da ake kawo wa arewa daga kudancin Nijeriya da ke Sabon garin Zariya, ya yi wannan yabo a lokacin da ya zanta da wakiln Leadership A YAU, a Zariya.
Alhaji Haruna Jega, wanda kuma aka fi sani da Alhaji Rabi’u Jega ya ci gaba da cewar, wannan mataki da gwamnatin tarayya ta dauka, zai yi maukar tasiri wajen bunkasa kasuwanci, kamar yadda Alhaji Rabi’u Jega ya ce, ba sana’ar kifi kawai ba, da kuma bunkasar sauran bangarorin kasuwanci da dama. Ya kara da cewar, wannan matsala ta bukatar jawo kogi daga kudanci zuwa arewacin Nijeriya, gwamnatocin baya sun yi alkawari ya fi shurin masaki, a cewar Alhaji Rabi’u Jega, haka gwamnatocin suke shudewa, ba tare da sun cika alkawarin da suka yi ba.
Alhaji Rabi’u Jega, wanda kuma tsohon shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ne na ma su sana’ar sayar da kifi a ‘’P/Z Sabon garin Zariya, ya bayar da misali da zuwa yanzu, gwamnatin tarayya ta fara jawo kogin daga kudancin Nijeriya zuwa jihohin Kabbi da kuma jihar Neja,Kamar yadda ya ce, an sami raguwar yawan kudaden da ‘yan kasuwa ke kashe wa wajen dauko kayayyakinsu daga kudanci zuwa arewa, saukin kuma, a cewar Alhaji Rabi’u Jega ya fara gangarawa ga al’umma da suke hulda da ‘yan kasuwan.
Sai dai kuma, fitaccen dan kasuwan kifin ya nunar da cewar, ya na da muhimmanci gwamnatin tarayya ta fadada wannan waje, ta yadda sauran ‘yan kasuwa da suke dauko kayayyakinsu daga kudancin Nijeriya za su rika amfani da wadannan tashoshi biyu, domin bunkasa harkokin kasuwancin da suke yi a arewa.
A karshe, Alhaji Rabi’u Jega, ya yi kira ga gwanonin jihohin arewa goma sha tara, da su fito da wasu tsare–tsare da za su tallafa wa ‘yan kasuwa da suke harkar kasuwanci daga kudancin Nijeriya zuwa jihohinsu, wannan mataki, a cewar Alhaji Rabi’u Jega tamkar sun tallafa wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ne na shirin da ya sa wa gaba, na bunkasa kasuwanci a jihohin da suke arewacin Nijeriya.
daga Shafin Leadership
0 komentar:
Post a Comment