‘Yan sanda sun damke wata ‘yar aiki bayan da ta ji wa maigidanta mummunan rauni a yayin da ya ke yunkurin yi mata fyade. Wannan lamari ya faru ne a kasar Uganda. ‘Yar aikin mai suna Nakayanga Rashida ta kwada wa maigidan na ta dutse ne a kai, lamarin da ya sanya shi ya yi ta zubda jini. Yayin da yan sanda suka sanya mata ankwa, Rashida ta yi ta zubar da hawaye ta na rokon a yafe mata, kamar yadda rahotan ya bayyana. Toh sai dai babu batun ko ‘yan sandan sun kama maigidan da yunkurin fyade ko kuwa kyale shi suka yi.





0 komentar:
Post a Comment