Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Jerin sunayen Mata Biyar Da Suka Fi Kudi A Duniya




Duk bahaushe da zaran an ce, masu gidan rana, ya san magana ce ta kudi. A zahiri yake ana kiransu ne da masu gidan rana kasantuwar sai an sha ranar ce ake samun su, domin ba a samun su kwance a daka. Sannnan kuma wani abin shi ne gogoriyon da ake yi a tsakanin al’umma wajen tara kudaden, wanda hakan ya sanya da bubba da yaro, mace da namiji kowa iyaka na shi kokarin ne yake yi.
Idan ana maganar dukiya, a kullum a kan sami jinsin Maza ne a sama, duk kuwa da cewa, ko a yanzun hakan, masu dukiya Goma da ke saman kowa a duniyar nan duk Mazan ne, kamar yadda yake a shafukan mujallar nan mai kammala kididdiga kan ire-iren wadannan lamura wacce ake kira da Forbes, amma duk da hakan, Matan suna ta kara matsowa dab da dab da jinsin na maza.
A bisa kididdigan da wannan mujallar ta Forbes, ta yi, Mata 256 sun shiga cikin jerin masu wadata a duniyar nan, ta hanyar kasantuwar su a jerin Bilyoniyoyi a a wannan shekarar ta 2018. Mujallar ta Forbes, ta taro jimlar abin da wadannan hamshakan masu kudin mata su 256 suka tara, wanda a kididdigan Mujallar, Matan masu dukiya a duniyan nan a wannan shekarar sun tara tsabar kudi sama da Dalar Amurka Triliyon daya, wanda za mu iya cewa ya haura Naira Triliyon 360 kenan idan muka canza su zuwa Nairar da muke kashewa. Wannan adadi na kudaden matan mawadata zalla, ya fi karfin kasafin kudin gwamnatoci masu yawa idan an hada su.
Yawancin dai wadannan Matan masu dukiya a duniyar nan, da mujallar ta samo sirrin tarin arzikin na su duk ‘yan kasuwa ne, masu Kamfanoni a kowane fanni.
Ga kuma lissafin su kamar haka:
1. Alice Walton

Alice Walton, a yanzun haka dai a wannan duniyar tamu, ita ce Matar da bincike ya tabbatar da cewa, ta fi kowace mace kudi a wannan duniyar. Alice Walton, ita ta zo na daya cikin mata a yawan dukiya a wannan shekarar ta 2018, sannan kuma a duk duniyar nan, idan an hada har ma da Mazan, ita ce ta 16, a tarin dukiya duk duniya.
Walton, hamshakiyar mai kudi, ita kadai ta tara tsibin dukiyar da ta kai mikidarin Naira Triliyon 16.5. Sannan kuma, mafiya yawan wannan dukiyar na ta, duk ta tara ta ne daga ribar da take samu na hannayen jarukan da take da su a shahararren kamfanin nan mai suna, Walmart, wanda Ubanta ne ya kirkiro tare da kafa Kamfanin na Walmart, watau, Sam Walton.

2. Francoise Bettencourt Meyer

Francoise Bettencourt Meyer, ita kuwa ta gaji tarin dukiyar na ta ne daga mahaifiyarta, L’oreal, bayan da mahaifiyar nata ta mutu tana da shekaru 94 da haihuwa.
Meyer, ta kasance mace ta biyu ne a wannan duniyar cikin mata mafiya tarin dukiya, domin kuwa an kiyasta tulin dukiyar nata wacce ta kai mikidarin Naira Triliyon 15.1, wacce kuma akalla kashi 33 cikin 100 na wannan tsugugin dukiya na ta, duk daga ribarta ne na hannun jarin da take da shi a kasurgumin Kamfanin nan mai yin kayan shafe-shafe na mata mai suna, L’oreal, da hakan ne ta kasance mace ta biyu mai yawan kudi a wannan duniyar a halin yanzun cikin wannan shekara ta 2018.

3. Sussane Klatten

Klatten, ita ce mace ta uku wacce ta fi kowace mace tarin dukiya yanzun haka a cikin duniyar nan bakidayanta. Ta kuma gaji wannan tulin arzikin ne daga hannayen jarin da ta gada a shahararren kamfanin nan mai kera Motocin BMW.
Ta sami zama a mataki na uku ne na macen da ta fi kudi a duniyar nan cikin wannan shekara ta 2018, da jimillan dukiyarta wacce ta kai Naira Triliyon Tara.

4. Jackueline Mars

Mars, ta yi kwaramniyar tara dukiyarta ne wacce ta kai har Naira Triliyon 8.2, ta hanyar hannayen jarin ta a kamfanin yin ababen tsotse-tsotsen nan na kasar Amurka mai suna, “Mars.”

Kakanta yana daya daga cikin attajiran da suka hadu suka kafa kamfanin mai yin kayan tsotse-tsotse.

Jackueline Mars, jika ce wajen sanannen attajirin nan na kasar Amurka mai suna, Frank C. Mars, wanda aka hakikance da cewa shi ne tushe kuma usulin kafa wannan shahararren kamfanin mai sarrafa kayan tsotse-tsotsen mai suna, Mars, wanda kayan kamfanin suka shahara suka kuma cika kusan ko’ina a cikin wannan duniyar tamu.

5. Yang Huiyan

Wannan mata ‘yar asalin kasar Sin, wacce kuma kamfanin ta na gine-gine ya shahara a kasar ta Sin, ita ce binciken Mujallan ta Forbes, ta binciko a matsayin mace ta biyar da ta kere duk wata mace a duniyar nan kudi a wannan shekara ta 2018.
An kiyasta dukiyar Huiyan, wacce ta haura kadan kan Naira Triliyon 7.8, da wannan yawan dukiya na ta ne kuma ta kasance macen da ta fi kowace mace dukiya a bakidayan nahiyar ta Asiya.

Huiyan, ‘yar shekaru 36, ita ce mace mafi karancin shekaru a duk cikin jerin wadannan mata biyar da suka fi dukkanin matan duniya kudi.

Share this


2 komentar:

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies