Hassana da Hussaina Musa Abdullahi, sune mafi mafi shaharar tagwaye a dandalin kannywood. An haife su kuma sun taso ne a jihar Kano, inda Hussaina ta makaranta koyon tsafta ta jihar Kano kuma take aiki a ma'aikatar kewaye ta jihar.
Ita kuwa Hassana tayi karatunta ne a makaranta koyon shari'a ta Mallam Aminu Kano, inda a yanuz duk su biyun suke ci gaba da sharar fage a shirin fina-finan hausa.
Tagwayen wanda saboda tsabar kama mutane da yawa basu iya banbancesu sun taka rawar gani a fina-finai sama da guda 30, inda suka fi shahara da kaurin suna a finan-finan Mairon Kauye da kuma Mizani.
Manunai a dandalin Kannywood sun bayyana irin zakakurancin wannan jarumai biyu bisa la'akari da yadda suke gwangwajewa a duk matakin da aka umarce su da taka rawar gani, inda suka bayyana wasu ra'ayoyinsu a wata ganawa da jaridar Daily Trust ta karshen wannan mako.
Hausazone.com ta fahimci cewa, a halin yanzu akwai sama da fina-finai 40 da jaruman suka fito a yayin da wasunsu sun shiga kasuwa wasu kuma na nan tafe. Ire-iren wadannan fina-finai sun hadar ‘Garba Gurmi Sabon Dan Tijjara’, ‘Duka Biyu’, ‘Rikita-Rikita’, ‘Duk Mace Macece’, ‘Fitsarin Fako’, da kuma ‘Ibro Dan Karota’.
A yayin tattaunawa da 'yan jarida, Hussaina ta bayyana cewa babu kamshin gaskiya dangane da rahotanni na cewar sai sun zabi irin fim din da suke bukatar fitowa, sai dai su kan duba irin shirin da ba zai kawo musu nakasun kima da zubuar musu da mutunci ba.
Take cewa, ko shakka babu sukan taimakawa junansu wajen shirin fim, musamman a wani lokaci da Hassana ke rubuta jarrabawa bata samu damar halartar karashe wani shiri sai ita ce ta karashe mata.
Tagwayen sun bayyana cewa, gaskiya ne suna da samarinsu wadanda basu da alaka da shirin fim kuma suna basu goyon bayan akan sana'arsu da suka sanya a gaba.
A yayin tuntubar tagwayen na cewar ko zasu ci gaba da wannan sana'a bayan sun shiga dakunan mazajensu, Hassana ta kada baki da cewar ta yiwu sai dai babu wanda ya san mai zai faru gobe.
0 komentar:
Post a Comment