Home

Music

Video

Kanny

Tags:

Wani Mutum Ya daure yarsa Cikin gida Tsahon shekara 3 akan auren Dole

Cikin Bidiyo
Daga Nasir Salisu Zango
GASKIYA ANA RASHIN IMANI: Ku kalli wannan bidiyon Allah ka takaita mana masifun Zamani, jiya muka Sami labarin wasu sun kona mutum da matarsa Mai tsohon ciki da yarsa Mai shekara .2
Yau kuma muka Gano wani mutum wanda ya daure 'ya'yansa biyu a gida tsahon shekaru 3 saboda sun yi masa wani laifi, har takai namjin ya mutu, a zuwa gaisuwa ne muka Gano macen kuma tuni an kubutar da ita shikuma mahaifinsu da matar sa suna hannun hukuma(yau zamu yi cikakken bayani a cikin shirye shiryen mu) to Amma Wai meke kawo ta azarar irin wadannan matsaloli ne?


A kwanakin baya wani ya shiga har gida ya yanka Abokin kasuwancinsa, saboda yana son cinye masa naira miliyan 3 da yake binsa bashi, Dan haka ya Kira shi cewar zaizo gida ya kawo masa kudin, Amma kasancenwar yasan cewar mutumin ya Sami sabani da matarsa, sai yayi amfani da damar ya Debo Yan ta adda suka yanka mutumin suka kuma rubuta cewar, Wai shine ya kashe kansa saboda Rikicin sa da matar sa, Amma da yake Allah shine Mai rayawa, kafin wannan mutum ya rasu, ya fito waje yayi ihu an kawo masa dauki kuma ya rubuta ainihin abin da ya faru, tuni har an kama masu wannan aika aika. Abin fa da ban tsoro matsalolin suna Yawaita, yakamata mu fara hada Kai domin Gano yadda zamu tunkari irin wadannan matsaloli maimakon tayar da jijiyar Kan abin da bashi ma da tasiri ga rayuwar mu.

Ga Bidiyon A kasa



Share this


0 komentar:

Post a Comment

Popular post

Arewa no.1 Hausa News Kannywood | All Rights Reserved
Fb tt wp ig g+
Owned And Design By Hausazone Technologies